Fiorentina ta nada sabon koci Sousa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sousa ya horar da QPR,da Swansea City da Leicester City

Kungiyar Fiorentina ta nada tsohon kocin QPR da Swansea, Paulo Sousa, a matsayin mai horar da 'yan wasanta.

Sousa, mai shekaru 44, dan kasar Portugal ya maye gurbin Vincenzo Montella wanda aka sallama daga aikin.

Kungiyar ta kori Montella ne bisa dalilin da ta ce bashi da da'a duk da jagorantar Fiorentina mataki na hudu a kan teburin Seria A da ya yi da hakan ya ba su gurbin buga Europa League a badi.

Sai dai kuma magoya bayan Fiorentina sun yi zanga-zanga kan daukar Sousa a matsayin kocin kungiyar, saboda ya buga wa Juventus wasanni tsawon shekaru biyu a baya.