Pirlo zai koma taka leda New York City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pirlo yana son ya koma taka leda a Amurka a New York City

Dan kwallon Juventus, Andrea Pirlo, yana tattaunawa da kulob din New York City domin ya koma buga tamaula a Amurka.

Har yanzu ba su cimma yarjejeniya ba, amma idan Pirlo ya koma can da murza leda zai fara wasa tare da Frank Lampard a karawar da za su yi da Toronto FC ranar 12 ga watan Yuli mai zuwa.

Sauran shekara daya kwantiragin Pirlo ta kare da Juventus, amma ya sanar da cewar yana son barin kulob din.

Pirlo mai shekaru 36 ya lashe kofunan Serie A shida a wasannin da ya buga wa AC Milan da Juventus.

Ya kuma dauki kofunan zakarun Turai guda biyu da AC Milan da kuma kofin duniya da ya lashe tare da tawagar kwallon kafar Italiya a shekarar 2006.