Liverpool ta amince ta dauki Roberto Firmino

Image caption Tuni Liverpool ta dauki 'yan wasa uku a bana

Liverpool ta amaince za ta dauki dan kwallon Brazil, Roberto Firmino, wanda ke murza leda a kulob din Hoffenheim kan kudi £29m.

Firmino mai shekaru 23, wanda ke buga wa tawagar kwallon kafar Brazil gasar Copa America da Chile ke karbar bakunci, zai kuma jira takarnar izinin da zai koma taka leda Ingila.

Babban jami'in Liverpool Ian Ayre yana kasar Chile, domin cigaba da tattaunawa da dan kwallon da ake hasashen zai saka hannu a Anfield tsawon shekaru biyar.

Tuni kungiyar Liverpool ta dauko dan wasan Burnley Danny Ings da mai tsaron raga Adam Bogdan da mai tsaron baya Joe Gomez da kuma James Milner.