Ana bincike kan gina filin West Ham

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption West Ham ta kare a mataki na 12 a kan teburin Premier bana

Tsohon shugaban Leyton Orient, Barry Hearn, ya bukaci a sanar da jama'a yarjejeniyar da West Ham ta kulla kan barin Boleyn Ground, domin koma wa filin wasa da ake kira Olympic Stadium.

An kiyasta cewa za a kashe £272m wajen gyaran filin wasan.

West Ham za ta bayar da tallafin £15m, amma wani rahoto da aka fitar ya ce kulob din zai biya kudin haya £2m a duk shekara, wanda kungiyar ba ta sanar wa al'umma ba.

Hearn ya ce "An boye hakikanin kudin aikin gina filin wasan, kuma magajin garin Landan ya ki fayyace yadda ake gudanar da aikin".

West Ham -- wacce ta kare a mataki na 12 a a kan teburin Premier bana -- tana kokarin komawa Olympic Stadium domin ci gaba da yin kakar wasannin 2016-17.

An gina filin wasa na Olympic Stadium --wanda ke kan titin Stratford-- wanda babu filin wasan kwallon kafa a cikinsa domin karbar bakuncin Landan Olympic a shekarar 2012.