Liverpool ya dauki Firmino a kan £29m

Image caption Firmino shi ne dan wasa na biyu mafi tsada da kulob din Liverpool ya saya.

Kulob din Liverpool ya dauki dan wasan gaba na Hoffenheim, Roberto Firmino tsawon shekaru biyar a kan £29m.

Sai dai kwantaragin da ya sanya wa hannu zai fara aiki ne bisa sharadin za a duba lafiyarsa idan ya dawo daga Chile, inda ya je domin wakiltar r Brazil a gasar Copa America.

Firmino, wanda ya zura kwallaye 47 a wasanni 151 da ya buga wa Hoffenheim, shi ne dan wasa na biyu mafi tsada da kulob din Liverpool ya saya.

Tuni kungiyar Liverpool ta dauko dan wasan Burnley Danny Ings da mai tsaron raga Adam Bogdan da mai tsaron baya Joe Gomez da kuma James Milner.