Ba a bani goron gayyata ba — Enyeama

Image caption Vincent Enyeama ya buga wa Super Eagles wasanni sama da 100

Mai tsaron ragar Super Eagles, Vincent Enyeama, ya ce ba a bashi goron gayyata zuwa gaban kwamintin ladabtarwa na NFF da suka zauna ranar Laraba ba.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta yi tunanin cewar Enyeama ya kunce yarjejeniyar da'ar 'yan wasan kwallon kafar kasar da suka kulla a baya.

Mai tsaron ragar ya yi jawabi ne a kan rashin tsaro a Kaduna, a lokacin da Super Eagles ta fafata da Chadi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Enyeama ya ce "Ina martaba kasarsa da dukkan jami'an da suke shugabantar hukumar kwallon kafar kasar, shi ya sa na ji maganganun da ake yi a kaina bambarakwai".

"A matsayina na kyaftin din tawagar Super Eagles ina da damar yin korafi a kan yanda 'yan wasa ke fargabar filin da za mu yi wasa, wanda hakan NFF ba ta ji dadin hakan ba".

Golan ya kuma ce hukumar ta umarce shi da ya nemi afuwa kan batun da ya yi, ya kuma yi hakan, amma "sai a kafar yada labarai na ji cewar ban je gaban kwamitin NFF ba."