Za'a kayata St George's Park

Hakkin mallakar hoto fa
Image caption An bude St Geaorge Park a shekarar 2012

An fara shirin gina filin wasan kwallon Golf a St George's Park domin kayata shi, bayan da Steven Gerrard ya yi korafi da cewar wurin yana gundurar jama'a.

Gerrard ya ce ginin na hukumar kwallon kafar Ingila, ba shi da abubuwan kayatarwa a wurin da zai dinga jan hankalin 'yan wasa.

Manajan daraktan wurin Julie Harrington ya ce an tanadi kayayyaki da za a saka a cibiyar da ke Staffordshire.

Jami'an St George's Park sun fara tattaunawa da hukumar gundumar yammacin Staffordshire Borough domin samun izinin gina katafaren filin wasa na Golf.

An bude St George's Park a ranar 9 ga watan Oktoban 2012.