Za'a binciki Jara kan jan katin Cavani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chile ce ta doke Uruguay da ci daya mai ban haushi

Mahukunta gasar Copa America za su binciki hatsaniyar da ta barke tsakanin mai tsaron bayan Chile Gonzalo Jara da Edinson Cavani a lokacin da suka fafata a ranar Laraba.

Chile wacce ke karbar bakuncin Copa America ce ta kara da Uruguay a wasan daf da na kusa da karshe a gasar.

A wani faifan bidiyo da aka nuna a akwatin talabijin dake filin wasan an ga Jara ya yi nuni da yatsansa ga bayan Cavani, wanda hakan alamune na cin zarafi da batanci.

Cavani ya fusata a inda ya zabga wa Jara mari bayan da alkalin wasa bai dauki mataki kan cin zarafin da aka yi masa ba, lamarin da alkalin wasa ya kore shi daga wasan.

A karshen karawar Chile ce ta kai wasan daf da karshe a gasar, bayan da ta samu nasara da ci daya mai ban haushi.