Keshi da Enyeama na jiran hukuncin NFF

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enyeama ya yi wa Super Eagles wasanni sama da 100

Stephen Keshi da Vincent Enyeama suna jiran hukuncin da hukumar kwallon kafar Nigeria NFF za ta yanke a kansu.

A ranar Talata kwamitin ladabtarwa na NFF ya zauna taro da Keshi kan jin dalilin da ya sa shi ya nemi aikin horar da 'yan kungiyar kwallon kafar Ivory Coast.

Enyeama bai halarci zaman ba ya kuma ce ba a ba shi goron gayyata ba domin amsa tuhuma a kan batun da ya yi a kan rashin tsaro a Kaduna.

Hukumar kwallon kafar Ivory Coast ce ta fitar da sunayen masu son horar da kasar tamaula ciki har da sunan Stephen Keshi.

Shi kuwa mai tsaron ragar Super Eagles ya yi jawabi ne kan rashin tsaro a Kaduna, a karawar da Nigeria ta yi da Chadi a wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Afirka.

A cikin watan Afirilu ne Keshi ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da NFF domin ya kara jagorantar Super Eagles.