An dakatar da Dempsey daga buga wasanni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dempsey ya amince da hukuncin da aka yanke masa

Hukumar kwallon kafar Amurka ta dakatar da Clint Dempsey daga buga US Open Cup har tsawon shekaru biyu, sakamakon yaga littafin alkalin wasa da ya yi a lokacin da ake fafatawa.

Dampsey mai taka leda a Seattle Sounders ya kwace littafin alkali Daniel Radford ya kuma kekketa shi bisa jan kati da aka bai wa abokin karawarsa a wasan.

Daga nan ne alkalin wasa ya kori Damsey daga fili lamarin da ya sa Seattle ta karasa wasan da 'yan kwallo bakwai a fili wanda tun farko an bai wa 'yan wasa uku jan kati.

A karshen wasan Portland Timbers ce ta doke Seattle Sounders da ci 3-1.

Dampsey, wanda aka dakatar daga buga wasannin Major League sakamakon laifin da ya aikata, ya ce ba zai daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke masa ba.