Cech ya kulla yarjejeniya da Arsenal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cech ya buga wa Chelsea sama da wasanni 300

Mai tsaron ragar Chelsea, Petr Cech, zai ziyarci Arsenal domin likitocin kungiyar su duba lafiyarsa, a shirye-shiryen da yake yi na son komawa can da taka leda.

Cech da Arsenal sun cimma matsaya kan kudin da za a bai wa golan mai shekaru 33 idan ya koma Gunners buga mata wasanni.

Mai tsaron ragar dan kwallon Jamhuriyar Czech shi ne zai zama dan wasa na farko da Arsenal za ta dauka a bana.

Cech ya koma murza leda ne Stamford Bridge daga kulob din Rennes na Faransa a shekarar 2004.

Ya kuma buga wa Chelsea wasanni sama da 300, yayin da ya lashe kofunan Premier hudu da kofin FA da League Cup guda uku da kofin Zakarun Turai da kuma na Europa.