Carlos Tevez ya koma Boca Juniors

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tevez ya lashe kofuna uku a Ingila sannan ya dauki guda biyu a Italiya

Dan kwallon Argentina Carlos Tevez ya kammala komawa Boca Juniors daga kulob din Juventus na Italiya.

Tevez mai shekaru 31, ya fara taka leda a matsayin kwararren dan wasa a Boca, yayin da ya bar kungiyar ya koma buga tamaula a shekarar 2004 a nahiyar Turai.

Tsohon dan wasan Manchester United da Manchester City da kuma West Ham ya zura kwallaye 20 a gasar Serie A da aka kammala a Juventus.

Tun a baya an yi ta hasashen cewar Tevez zai koma taka leda a Liverpool ko Atletico Madrid ko kuma Paris St-Germain.

Tuni Juventus ta maye gurbin Tavez, a inda ta dauko Mario Mandzukic daga Atletico ta Spaniya.