Giwa FC za ta kara da El-Kanemi a Kaduna

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na 14 a gasar Premier Nigeria

Kungiyar Giwa FC za ta fafata da El-Kanemi Warriors a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 15 da za su buga a Kaduna.

Sauran wasannin da za a yi sun hada da karawa tsakanin FC Ifeanyiubah da Wikki Tourists da kuma yin gumurzu tsakanin Enyimba da Nasarawa United a garin Aba.

Sunshine Stars wacce ke mataki na daya a kan teburi za ta ziyarci Rangers, a inda Kano Pillars za ta karbi bakuncin Dolphins ta Fatakwal.

Ga wasannin mako na 15 da za a buga:

  • Giwa FC vs El-Kanemi Warriors
  • FC Ifeanyiubah vs Wikki Tourists
  • Sharks vs Heartland
  • Enyimba vs Nasarawa United
  • Bayelsa United vs Kwara United
  • Lobi Stars vs Abia Warriors
  • Akwa United vs Warri Wolves
  • Rangers vs Sunshine Stars
  • Kano Pillars vs Dolphins