Phil Neville na tattaunawa da Valencia

Image caption Phil Neville yanzu yana yin aikin sharhin wasanni ne a talabijin

Phil Neville na tattaunawa da Valencia don karbar aikin mataimakin kociya, wanda kulob din ya sanar da cewar ya dauki Neville aikin.

Kulob din Valencia mai murza leda a Spaniya ya saka a shafinsa na intanet cewar ya dauki Phil Neville a matsayin mataimakin koci.

Neville ya shaidawa BBC cewar suna tattaunawa kan batun, kuma da sauran batutuwan da ba su cimma ba, kafin su kulla yarjejeniya a nan gaba.

Tsohon dan wasan Manchester United da Everton ya yi aikin mataimakin David Moyes a lokacin da ya horar da United.

Neville zai maye gurbin Scot Ian Cathro, wanda zai koma aiki Ingila tare da Steve McClaren a Newcastle United.