An yi kira da Blatter ya martaba ikirarinsa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Blatter ya ce zai sake yin takarar kujerar Fifa a zaben gaba

An yi kira ga shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Sepp Blatter da ya martaba ikirarin da ya yi cewar zai yi murabus daga shugabantar hukumar.

Domenico Scala jami'in da ke shugabantar Fifa kan binciken kudi da tabbatar da an kashesu bisa kan ka'ida ne ya yi wannan kiran.

Ranar 2 ga watan Yuni ne Blatter ya ce zai yi murabus daga shugabancin Fifa daga tsakanin Disamba zuwa Maris a lokacin babban taron hukumar da ta gudanar.

Sai dai kuma a ranar Alhamis, Blatter ya yi amai ya lashe, har ma ya kara da cewar zai tsaya takarar shugabancin hukumar da za a sake yi.

Scala ya ce "Lokacin yin barkwanci ya wuce, ya kamata Blatter ya sauka daga kan mulki domin a zabi sabon shugaban da zai dawo da martabar Fifa".

Hukumar ta Fifa ta shiga rikita-rikitar cin hanshi da rashawa, a inda mahukunta suka damke wasu jami'ai bakwai da ake zargi da karbar na goro.