Tunisia ta sallami kocinta Leekens

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leekens ya yi aiki a Turkiya da Algeria da Netherlands da kuma Saudi Arabia.

Hukumar kwallon kafar Tunisia ta sanar da sallamar kociyanta George Leekens daga aikin.

Tunisia ta yi hakan ne makwanni biyu da Leekens ya jagoranci kasar da ta doke Djibouti da ci 8-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Leekens ya jagoranci Tunisia a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015 a Equatorial Guniea zuwa wasan daf da na kusa da karshe.

Hukumar kwallon kafar Tunisia ta sanar da korar Leekens daga aikinsa a kan shafinta na intanet.

Tunisia za ta ziyarci Liberia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka a cikin watan Satumba.