Arsenal ta dauki golan Chelsea Petr Cech

Hakkin mallakar hoto arsenal
Image caption Petr Cech shi ne dan wasan farko da Arsenal ta dauko a bana

Arsenal ta dauki mai tsaron ragar Chelsea, Petr Cech, a yarjejeniyar shekaru hudu kan kudi £10m.

Cech golan Jamhuriyar Czech ya buga wa Chelsea wasanni sama da 400 a tsawon shekaru 11 da ya yi a Stamford Bridge.

Mai tsaron ragar mai shekaru 33 ya buga wasannin Premier guda Shida, yayin da Thibaut Courtois ya maye gurbinsa a wanda yake kamawa Chelsea Tamaula.

Golan ya koma murza leda ne Stamford Bridge daga kulob din Rennes na Faransa a shekarar 2004.

Cech shi ne dan wasan farko da Arsenal ta dauka a bana, kuma zai fuskanci Chelsea a karawar da za su yi da Arsenal a gasar Community Shield a Wembley ranar 2 ga watan Agusta.

Arsenal wacce ta dauki kofin FA, tana yin amfani da mai tsaron raga ne tsakanin Wojciech Szczesny ko kuma David Ospina a wasannin da take yi.