Man United ta taya Ramos na Real Madrid

Image caption Real Madrid ba ta nuna alamun za ta tsawaita kwantiragin Ramos ba

Manchester United ta taya dan kwallon Real Madrid, mai tsaron baya Sergio Ramos kan kudi £28.6m.

United na hangen Ramos zai iya barin Madrid bayan da ta ki tsawaita kwantiraginsa da zai kare da kulob din a karshen kakar wasannin 2017.

Ramos dan kwallon tawagar Spaniya ya buga wa Madrid wasanni 445, tun lokacin da ya koma Bernabeu daga Sevilla a shekarar 2005.

United tana neman mai tsaron baya da zai sa ta kara yin fice a badi, ganin yadda ta kare a mataki na hudu a kan teburin Premier a bana.

Ramos ya buga wa Spaniya wasanni sau 128, yayin da ya lashe kofin nahiyar Turai da kasar a shekarar 2008 da 2012 da kuma kofin duniya a shekarar 2010.