Djokovic ya fara kare kambunsa a Wimbledon

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Djokovic ya fara kare kambunsa da kafar dama a Wimbledon

Mai rike da kofin kwallon tennis ta Wimbledon, Novak Djokovic, ya fara kare kambunsa, a inda ya doke dan kasar Jamus Philipp Kohlschreiber a ranar Litinin.

Djokovic dan kasar Serbia ya lashe wasan ne da ci 6-4 da 6-4 da kuma 6-4, kuma da wannan nasarar da ya samu zai kara da Lleyton Hewitt ko kuma Jarkko Nieminen a wasan zagaye na biyu.

Wannan ne karon farko da Djokovic ya buga babbar gasa tun bayan da ya yi rashin nasara a hannun Stan Wawrinka a wasan karshe a gasar French Open.

Djokovic ya dan samu tsaiko a karawar a inda ya yi kura-kurai sau 20 kafin daga baya ya lashe fafatawar.