Za a buga wasan karshe a filin Millennium

A filin ne aka buga wasan Super Cup a 2014 a inda Madrid ta doke Sevilla

Asalin hoton, new evans picture agency

Bayanan hoto,

A filin ne aka buga wasan Super Cup a 2014 a inda Madrid ta doke Sevilla

Hukumar kwallon kafar nahiyar Turai ta sanar da cewar filin wasa na Cardiff Millennium ne zai karbi bakuncin wasan karshe na cin kofin zakarun Turai na 2017.

Za a buga wasan ne ranar Asabar 3 ga watan Yuni, yayin da a gasar wasannin mata za su fafata a wasan karshe kwanaki biyu kafin wasan maza.

Filin mai daukar 'yan kallo 74,500 ya taba karbar bakuncin wasan karshe na kofin FA da League Cup da Community Shield daga tsakanin shekarun 2001 zuwa 2006.

Haka kuma filin ya karbi bakuncin wasan karshe na Super Cup a shekarar 2014, a inda Real Madrid ta doke Sevilla, kuma ya karbi wasannin Olympics a shekarar 2012.