Bility zai bar wa Hayatou takarar Fifa

Image caption Bility ya fara shugabantar hukumar kwallon kafar Liberia a shekarar 2010

Shugaban hukumar kwallon kafar Liberia Musa Bility ya ce zai janye daga takarar shugabancin Fifa, idan har Issa Hayatou ya ce zai nemi kujerar.

Bility ya sanar da cewa zai yi takarar kujerar Fifa a watan Yuni, bayan da Sepp Blatter ya ce zai yi murabus daga shugabantar hukumar kan zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye hukumar.

Bility ya shaida wa BBC cewar idan har shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Issa Hayatou ya ce zai tsaya takarar kujerar Fifa, zai janye aniyarsa nan take.

Shugaban hukumar kwallon kafar Liberia mai shekaru 48, shi ne mutum na biyu da ya nuna aniyar zai yi takarar kujerar Fifa, bayan Zico na Brazil.

Haka kuma Bility shi ne na biyu a Afirka da zai yi zawarcin kujerar bayan Hayatou da ya sha kaye a hannun Blatter a shekarun 2002, a lokacin zaben shugaban hukumar.