Bayern Munich ta dauki Douglas Costa

Hakkin mallakar hoto bayernmunich
Image caption Douglas Costa ya taka rawa a gasar kasar Ukraine

Bayern Munich ta Jamus ta dauki dan kwallon Brazil, Douglas Costa daga kulob din Shakhtar Donetsk.

Costa mai shekaru 24, ya saka hannu kan kwantiragin shekaru biyar kuma kan kudi £21m in ji Shakhtar ta Ukraine.

Dan wasan ya ci kwallaye 29 daga wasanni 149 da ya buga a Shakhtar, yayin da ya lashe kofin gasar kasar sau biyar.

Costa wanda ya buga wa Brazil gasar Copa America ya ce "Mafarkinsa ne ya zama gaskiya, kuma ya yi murna da zai murza leda a Jamus da Munich".