Clyne ya sa hannu a kwangila da Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nathaniel Clyne

Liverpool ta sanya hannu a yarjejeniya tare da Nathaniel Clyne wanda ta dauko daga Southampton a kan fan miliyan 12 da rabi.

Dan shekaru 24, ya amince da kwantaragin shekaru biyar domin taka leda a Anfield.

Clyne ya ce "Na ji dadin wannan abu, buri na ya cika domin na shiga cikin tarihi."

Ya kasance dan kwallo na shida da Liverpool ta dauko a cikin wannan bazarar.

Clyne ya hade da Roberto Firmino da Danny Ings da James Milner da Joe Gomez da kuma Adam Bogdan.