Wikki za ta karbi bakuncin Giwa a gasar Premier

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na 15 a gasar Premier Nigeria

Wikki Tourists za ta kara da Giwa FC a ci gaba da gasar Premier Nigeria wasannin mako na 15 ranar Laraba.

A ranar lahadi Wikki ta hada maki 26 a kan teburin Premier, bayan da ta doke Ifenyi Uba da ci daya mai ban haushi, yayin da Giwa FC ta casa El-Kanemi Warriors da ci 3-1 a Kaduna.

Sauran wasannin da za a buga El-Kanemi Warriors za ta fafata da Dolphins, yayin da Enyimba za ta ziyarci Kwara United da kuma wasa tsakanin Nasarawa United da Taraba FC.

Kano Pillars wacce ta buga 2-2 da Dolphins a Kano a wasan mako na 14 za ta ziyarci Enugu Rangers, a inda za a yi gumurzu tsakanin Heartland da Ifenyi Uba.

Ga wasannin mako na 15 da za a buga:

  • El-Kanemi Warriors - Dolphins FC
  • Wikki Tourists - Giwa FC
  • Heartland FC - Ifeanyi Uba
  • Shooting Stars FC - Sharks
  • Nasarawa United FC - Taraba FC
  • Kwara United - Enyimba Aba
  • Abia Warriors FC - Bayelsa United
  • Warri Wolves - Lobi Stars
  • Sunshine Stars - Akwa United
  • Enugu Rangers - Kano Pillars