Enyimba ta doke Kwara United 3-2 har gida

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin mako na 15 a gasar Premier Nigeria

Kungiyar Kwara United ta yi rashin nasara a hannun Enyimba International har gida da ci 3-2 a gasar Premier Nigeria wasan mako na 15 da suka yi ranar Laraba.

Da wannan nasarar da Enyimba ta samu ya sa ta yi kankankan da Sunshine Star wacce ta doke Akwa United 3-1 da maki 29 a kan teburin Premier.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Wikki Tourists ta garin Bauchi ta buga kunnen doki da Giwa FC, yayin da Shooting Stars ta doke Sharks da ci daya mai ban haushi.

Enugu Rangers ta hada maki uku a karawar da ta doke Kano Pillars da ci 2-1, a inda El-Kanemi ta zura wa Dolphins ta Fatakwal kwallo daya mai ban haushi a raga.

Ga sakamakon wasannin mako na 15 da aka buga:

  • El-Kanemi Warriors 1-0 Dolphins
  • Wikki Tourists 1-1 Giwa FC
  • Heartland 1-0 FC Ifeanyiubah
  • Shooting Stars 1-0 Sharks
  • Nasarawa United 2-0 FC Taraba
  • Kwara United 2-3 Enyimba
  • Abia Warriors 3-1 Bayelsa United
  • Warri Wolves 1-0 Lobi Stars
  • Sunshine Stars 3-1 Akwa United
  • Rangers 2-1 Kano Pillars