Mba ya koma Yeni Malatyaspor ta Turkiya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunday Mba ya fara haskakawa a gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a shekarar 2013

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, Sunday Mba, ya koma kungiyar Yeni Malatyaspor ta Turkiya daga CA Bastia ta Faransa.

Kungiyar Yeni Malatyaspor za ta buga gasar dake bin babbar gasar kasar Turkiya, bayan da ta samu tikiki a kakar wasannin bara.

Mba mai shekaru 26 ya koma murza leda CA Bastia ta Faransa a watan Janairun 2014 daga kulob din Warri Wolves na Nigeria.

Dan kwallon ya samu tsaiko a buga tamaula tun lokacin da ya ci kwallon da Super Eagles ta dauki kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013.

Tun daga lokacin ne Mba bai samu buga wa Nigeria wasanni da dama ba, har ma Super Eagles ba ta gayyace shi gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil ba.