Swansea ta dauki Eder na Sporting Braga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Swansea za kuma ta dauki dan wasa mai zura kwallo a raga kafin a fara Premier bana

Kungiyar Swansea ta dauki dan wasan Sporting Braga, Eder, sai dai ba ta sanar da kudin da ta sayo dan kwallon ba.

Eder mai shekaru 27 dan kwallon Portugal, ya kulla yarjejeniyar shekaru uku a Liberty Stadium.

Dan wasan ya buga wa tawagar kwallon kafar Portugal wasanni 18, ya kuma ci kwallaye 10 daga wasanni 29 da ya buga wa Braga a 2014-15.

Eder shi ne dan wasa na hudu da Swansea ta dauka a bana, bayan Andre Ayew daga Marseille da Franck Tabanou daga St-Etienne da kuma mai tsaron ragar Heerenveen Kristoffer Nordfeldt.

Haka kuma Swansea ta fara tattaunawa da dan kwallon Barcelona mai shekaru 18 Guillermo Lara.