Murray ya kai wasan zagaye na 3 a Wimbledon

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murray zai buga wasan zagayen gaba a ranar Asabar

Andy Murray ya kai wasan zagaye na uku a gasar kwallon tennis ta Wimbledon, bayan da ya doke Robin Haase na Netherlands.

Murray ya lashe wasan ne da ci 6-1 6-1 6-4, zai kuma kara a wasan gaba da Andreas Seppi na Croatian ko kuma Borna Coric a ranar Asabar.

Haase wande ke mataki na 78 a jerin 'yan wasan da suka fi iya kwallon tennis a duniya shi ne ya fitar da Murray a gasar a shekarar 2008.

Haka suma James Ward da Aljaz Bedene sun kai wasan zagayen gaba a gasar.