Atletico ta amince ta dauki Martinez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Martinez shi ne kan gaba a gasar Portugal a yawan cin kwallaye a shekaru uku a jere

Kungiyar Atletico Madrid ta amince za ta dauki dan kwallon Colombia Jackson Martinez daga Porto kan kudi £24.8m.

An yi ta rade-radin cewar Martinez zai koma taka leda a Arsenal, sai dai Porto ta sanar da cewar Atletico ta amince ta biya kudin yarjejeniyar da dan wasan ya kulla da ita.

Martinez mai shekaru 28, ya koma Porto a shekarar 2012, yayin da ya ci kwallaye 67 a wasanni 90 da ya yi, kuma shi ne kan gaba wajen yawan cin kwallaye a shekaru uku a jere a gasar Portugal.

Dan kwallon zai maye gurbin Mario Mandzukic a Atletico, wanda ya koma Juventus da taka leda.

Shi kuwa Mandzukic ya maye gurbin Carlos Tevez wanda ya koma kulob din da ya fara buga wa tamaula Boca Juniors na Argentina.