Hernandez ya karye a allon kafada

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hernandez ya je Real Madrid wasa aro a kakar wasan bara

Javier Hernandez ba zai buga wa Manchester United wasannin farko na kakar bana ba, bayan da ya karya allon kafadarsa a lokacin da yake yi wa Mexico wasa.

Hernandez ya ji raunin ne a lokacin da Mexico ke karawa da Honduras a gasar Gold Cup a Houston, kuma zai yi jinyar makwanni hudu.

Dan wasan, mai shekaru 27, ya ci kwallaye 59 a wasanni 154 da ya buga wa United, kuma watakila zai bar kulob din a bana.

A kakar bara Hernandez ya buga wa Real Madrid wasanni aro, daga karshen zaman da ya yi a Spaniya Madrid ba ta nuna sha'awar daukar dan wasan ba.