Odemwingie ya tsawaita kwantiragi a Stoke City

Hakkin mallakar hoto Phil Greig
Image caption Dan wasan ya kuma buga tamaula a Lille da kuma Lokomotiv Moscow

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, Peter Odemwingie ya tsawaita kwantiragin ci gaba da murza leda a kulob din Stoke City zuwa shekara daya.

Odemwingie zai ci gaba da wasa a Stoke City zuwa karshen kakar wasan badi, tare da yarjejeniyar za a iya kara tsawaita zamansa a kulob din.

Dan wasan ya yi fama da jinyar raunin da ya ji a gwiwarsa, dalilin da ya sa kenan bai buga wasanni akai-akai a kakar wasan da aka kammala ba.

Odemwingie tsohon dan kwallon West Bromwich Albion ya koma Stoke ne daga Cardiff City a shekarar 2014.

Haka kuma raunin da dan kwallon ya yi fama da jinya ya sa bai wakilci Nigeria ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ta dauka a shekarar 2013.