Amurka ta bukaci a mika mata jami'an Fifa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Yuni Sepp Blatter ya ce zai yi murabus daga shugabantar Fifa

Amurka ta bukaci Switzerland da ta mika mata jami'an Fifa bakwai da aka damke a watan Mayu kan zargin cin hanci da rashawa.

Manyan jami'an Fifa bakwai da aka kama a Zurich, suna daga cikin wakilan hukumar su 14 da ake zargi da yin almundahana da halalta kudaden haram da cin hanci da rashawa.

An zargin jami'an ne bayan da hukumar bincike ta Amurka ta yi wani bincike kan hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa.

Jami'an tsaron Zurich sun ce za su saurari mahukuntan Fifa bakwai da aka damke kan batun a maida su Amurka domin ta tuhume su.

Lauyoyin jami'an da ake zargi suna da kwanaki 14 da za su daukaka kara kan bukatar da Amurka ta gabatar na a mika mata su.