Zan kawo Pogba Barcelona— Laporta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manyan kungiyoyi na zawarcin Pogba

Dan takarar shugabancin kungiyar Barcelona Joan Laporta ya ce zai dauko dan wasan Juventus Paul Pogba idan har ya lashe zabe.

Rahotanni sun ce Barca ta taya dan kwallon Faransan mai shekaru 22, wanda ya taimaka wa Juve ta lashe gasar Serie A a kakar wasan da ta wuce.

"Akwai dan kwallon da muke so - Paul Pogba," in ji Laporta.

Kafafen yada labarai a Spain da Italiya sun ce Barca ta ba da tayin Euro miliyan 80 a kan Pogba wanda tsohon dan wasan Manchester United ne.

Laporta wanda ya jagoranci Barcelona daga shekarar 2003 zuwa 2010, shi ne ya dauko dan Brazil Ronaldinho da kuma Samuel Eto'o.