United ta yi zawarcin Schneiderlin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Southampton ta ce ba ta taba tunanin United za ta taya dan wasan ba, domin tana bukatarsa matuka

Southampton ta ki sallama Morgan Schneiderlin ga Manchester United da ta yi zawarci in ji Ronald Koeman.

Schneiderlin mai shekaru 25, bai halarci atisayen da Southampton ta yi a ranar Litinin, bisa rashin lafiya da ya yi fama da yi ba.

Koeman ya shaida wa BBC cewar United ta bukaci daukar Schneiderlin a makwonni biyu da suka wuce, yayin da muka ki sallama mata dan kwallon.

Schneiderlin ya fara buga wa Southampton tamaula a shekarar 2008, yayin da ya buga mata wasanni 261.

United na fatan za ta dauki dan wasan kafin ta tafi wasannin atisaye a Amurka ranar 13 ga watan Yuli.