Nani ya koma murza leda Fenerbahce

Image caption Nani ya koma wasa aro a Portugal a kakar wasannin bara

Dan wasan Manchester United, Nani, ya koma kungiyar Fenerbahce ta Turkiya kan kwantiragin shekaru uku kan kudi £4.25m.

Nani mai shekaru 28, ya ci wa United kwallaye 40 daga wasanni 229 da ya buga tun lokacin da ya koma Old Trafford daga Sporting Lisbon a shekarar 2007.

Dan kwallon ya buga wasa aro a Sporting Lisbon a bara, yayin da ya ci kwallaye 11.

Nani wanda ya tsawaita kwantiraginsa da United a watan Satumbar 2013, ya lashe kofunan Premier hudu da kofin zakarun Turai tun komawarsa Old Trafford.

Dan kwallon zai buga tamaula tare da abokan wasansa na tawagar kwallon kafar Portugal da suka hada da Raul Meireles da Bruno Alves a Fenerbahce.