Phil Neville ya fara aiki da Valencia

Hakkin mallakar hoto fizzeris
Image caption Neville tsohon dan kwallon Everton, ya yi aiki da David Moyes a Manchester United

Tshohon dan kwallon Ingila da Manchester United, Phil Neville, ya fara aikin mataimakin kocin Valencia.

Neville mai shekaru 38, ya fara aikin ne a ranar litinin, yayin da kungiyar ke shirin atisayen tunkarar gasar bana da za ta yi a Austria.

Valencia ta kammala a mataki na hudu a gasar La Ligar Spaniya bara , hakan ne yasa za ta buga wasan neman gurbin shiga gasar kofin zakarun Turai a watan Agusta.

Tsohon dan wasan Manchester United da Everton ya yi aikin mataimakin David Moyes a lokacin da ya horar da United.

Neville ya maye gurbin Scot Ian Cathro, wanda zai koma aiki Ingila tare da Steve McClaren a Newcastle United.