Barcelona ta dauko Turan daga Atletico

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arda Turan ya haskaka a Atletico Madrid

Barcelona ta dauko dan kwallon Turkiya Arda Turan daga Atletico Madrid a kan fan miliyan 24.

Dan kwallon mai shekaru 28 ba zai samu damar buga wa Barcelona kwallo ba har sai watan Junairun 2016 saboda Fifa ta dakatar da Barca daga sayen 'yan kwallo.

Ya zura kwallaye 22 a kakar wasanni hudu tare da Atletico tun bayan da ya bar Galatasaray a shekarar 2011.

A kakar wasan da ta wuce Barcelona karkashin jagorancin Luis Enrique ta lashe kofuna uku watau na La Liga da Copa del Rey da kuma na Zakarun Turai.

Bayaga Turan, Barca ta dauko Aleix Vidal daga Sevilla a kan fan miliyan 16.