Sterling ne matashin da ya fi daraja a Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Raheem Sterling ya ki tsawaita kwantiragi a Liverpool

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewar dan wasan Liverpool, Raheem Sterling, shi ne matashin dan kwallo da ya fi daraja a nahiyar Turai.

Soccer 20 Football Value Index ne ya ce Sterling wanda Liverppol ta ki sallama tayin da Manchester City ta yi wa dan wasan, ya kai darajar kudi £35m.

Dan wasan Manchester United Luke Shaw yana mataki na tara, yayin da John Stone na Everton ke matsayi na 16, a inda Calum Chambers na Arsenal ne na 19 a rahoton.

Binciken an gudanar da shi ne kan 'yan wasan da ke da shekaru 21 da suke murza leda a nahiyar Turai.

An kayyade darajar 'yan wasan ne bisa shekaru da kungiyar da suke buga wa tamaula da kunshin yarjejeniyar da suka kulla da yawan wasannin da suke buga wa kasashensu wasanni da kwallayen da suke ci da jin rauni da kuma jinya da sauransu.