NFF za ta dauki Oliseh kocin Nigeria

Image caption Oliseh ya buga wa Super Eagles wasanni 54 daga shekarar 1993 zuwa 2002

BBC ta fahimci cewar hukumar kwallon kafar Nigeria na tattaunawa da Sunday Oliseh kan aikin horas da tawagar kwallon kafar kasar.

A ranar Lahadi ce NFF ta sallami Stephen Keshi daga aikin, bisa samun sa da laifin zawarcin kocin Ivory Coast alhali yana da kwantiragi da hukumar kwallon kafar Nigeria.

NFF ce ta tuntubi Oliseh wanda yake da lasisin horas da tamaula na hukumar kwallon kafar Turai, domin ya maye gurbin Keshi.

Salisu Yusuf ne ke jagorantar Super Eagles a matsayin kocin rikwon kwarya, yayin da Shaibu Amodu ke saka ido kan yadda ake gudanar da tawagar.

Oliseh, tsohon kyaftin din Super Eagles yana daga cikin tawagar 'yan wasan kasar da suka lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994 da lambar zinare a wasannin Olympic a shekarar 2006.