An ci fenariti 36 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto leaguemanagementtwitter
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na 17 ranar Laraba

Bayan da aka buga wasannin mako na 16 a gasar Premier Nigeria, an ci kwallaye 36 a bugun fenariti 41 da alkalan gasar suka bayar.

Kungiyar Enyimba ce ta fi samun yawan fenariti a gasar, inda ta samu guda hudu ta kuma zura su a raga.

Jumulla an ci kwallaye 326 daga wasanni 157 da aka buga, bayan da aka kammala wasannin mako na 16 a gasar.

Sunshine Stars wacce ke mataki na daya a teburi da maki 30, ta fi yawan zura kwallaye a gasar, a inda ta zura 25 a raga.

Kungiyar Taraba FC wacce ke matsayi na 20 a teburin Premier, ta ci kwallaye 14 kacal, yayin da aka ci ta kwallaye 21 a gasar.