Bentaleb ya tsawaita kwantiragi a Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nabil Bentaleb dan wasan tawagar kwallon kafar Algeria

Dan kwallon Tottenham, Nabil Bentaleb ya tsawaita kwantiragin ci gaba da murza leda tsawon shekaru biyu da kulob din.

Bentaleb dan wasan Algeria, mai shekaru 20, ya koma Tottenham tala leda a watan Janairu a shekarar 2012, bayan da ya yi wasannin gwaji a White Hart Lane.

Dan kwallon ya fara buga wa Tottenham wasa a karawar da suka doke Southampton a gasar Premier a watan Disambar 2013.

Bentaleb wanda ya buga wa Algeria gasar cin kofin duniya a Brazil, ya yi wa Tottenham wasanni 35 ya kuma ci kwallo daya tak.