Emeniki zai maye gurbin Gyan a Al Ain

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Emenike dan kwallon tawagar Nigeria
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gyan ya ci kwallaye 95 daga wasanni 83 da ya buga wa Al Ain

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, Emmanuel Emenike, na daf da maye gurbin Asamoah Gyan, wanda zai koma China murza leda.

Kulob din Al Ain ya amince da tayin da kungiyar Shanghai SIPG ta yi wa Gyan, wacce tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson ke horas wa.

Gyan dan kwallon Ghana mai shekaru 29, ya ziyarci China domin duba lafiyarsa a ranar Laraba.

Emenike zai je hadaddiyar daulal Larabawa ranar Alhamis domin kammala yarjejeniyar da zai buga wasa aro a Al Ain daga Fenerbahce.

A kuma kunshin yarjejeniyar da Emeniki zai saka hannu, Al Ain za ta iya sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani a kungiyar.