United na daf da daukar Matteo Darmian

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United za ta fara wasan Premier da Aston Villa ranar Juma'a

Manchester United na fatan dauko dan kwallon Torino, Matteo Darmian, kan lokaci domin ya halarci atisayen da za ta yi a Amurka.

Dan wasan mai shekaru 25, mai tsaron baya, zai kuma iya buga wasa daga gaban masu tsaron bayan, ya kuma buga wa Italiya wasannin kofin duniya da aka yi a Brazil.

Zuwa yanzu Memphis Depay United ta dauko kan kudi £31m, kuma za a gabatar da shi a gaban 'yan jaridu a ranar Juma'a.

Har yanzu babu karin bayanai kan musaya tsakanin Golan United David De Gea da Sergio Ramos mai tsaron bayan Real Madrid.

United ta ci gaba da yin zawarcin Morgan Schneiderlin na Southampton, wanda aka ki sallama mata shi a makwonni biyu da suka wuce.

Manchester United za ta ziyarci Amurka domin yin atisayen tunkarar kakar wasannin bana a ranar Litinin.