Guardiola ya so aikin horas da Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kofuna 14 Guardiola ya lashe a Barcelonar Spaniya

Kociyan Bayern Munich Pep Guardiola ya so a ba shi ragamar horas da tawagar kwallon kafar Brazil a gasar kofin duniya da ta karbi bakunci a shekarar 2014, in ji Dani Alves.

Alves ya kara da cewa Guardiola ya dade da tsara yadda Brazil za ta dauki kofin duniya a 2014 da an ba shi aikin.

Sai dai Alves ya ce an samu cikas ne daga mahukuntan kwallon kafar kasar, bayan da suka yi fargabar dauko mai horas da tamaula daga waje.

Guardiola ya lashe kofuna 14 a shekaru hudun da ya yi a Barcelona ciki har da kofunan zakarun Turai guda biyu da ya lashe a Nou Camp.

Daga nan ne ya koma Bayern Munich a watan Yunin 2012, ya kuma dauki kofin Bundesliga biyu da Munich din.