Tottenham ta dauki Toby Alderweireld

Image caption Southampton ce ta so daukar Toby Alderweireld tun farko

Kungiyar Tottenham ta dauki Toby Alderweireld daga Atletico Madrid kan kwantiragin shekaru biyar.

Toby Alderweireld mai shekaru 26, dan kwallon Belgium ya buga wa Southampton wasannin Premier 26 aro a kakar badi.

Southampton tana son daukar matakin shari'a kan Tottenham domin tana da damar sayen dan kwallon kan kudi £6.8m a kunshin yarjejeniyar da ya buga mata wasa aro.

A yarjejeniyar sai idan Atletico ta biya kudi £1.5m ga Southampton kan Alderweireld, shi ne yake da damar taka leda da wata kungiyar.

Alderweireld ya buga wa Belgium wasanni 47, kuma zai murza leda a White Hart Lane tare da abokan wasansa a kasarsa da suka hada da Nacer Chadli da Mousa Dembele da kuma Jan Vertonghen.