Schweinsteiger ya yi murna da ake zawarcinsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sauran kwantiragin shekara daya ya rage wa dan kwallon a Munich

Dan kwallon Bayern Munich Bastian Schweinsteiger yana cike da faranciki da kulob din Ingila ke zawarcin ya buga masa tamaula in ji Karl-Heinz Rummenigge.

Sauran kwantiragin shekara daya da Schweinsteiger ya kulla da Munich ya kare, wanda ake rade-radin cewar zai koma taka leda Manchester United.

Rummenigge ya ce dan kwallon bai boye murnar da yake yi kan yadda United ke son ya buga mata wasa ba.

Dan kwallon ya buga wasa karkashin koci Louis van Gaal a lokacin da ya horas da Bayern Munich.

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola na fatan Schweinsteiger zai yanke shawarar kan makomarsa a kulob din nan ba da dadewa ba