Nigeria ta kara yin kasa a jerin Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta koma mataki na 10 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka

Tawagar Super Eagles ta Nigeria ta kara yin kasa a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka da Fifa ta fitar na watan Yuli.

Nigeria ta koma mataki na goma a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka, kuma ta 57 a duniya a jerin da Fifa ta fitar.

A watan Yuni da ya gabata Nigeria tana matsayi na bakwai a Afirka kuma ta 43 a duniya a jerin kasashen da suka fi yin fice a buga tamaula.

Kasar Algeria dai ta ci gaba da zama a mataki na daya a nahiyar Afrika ta kuma koma matsayi na 19 a jerin kasashen da Fifa ta fitar a watan na Yulin.

Ivory Coast wacce ta dauki kofin nahiyar Afirka a bana, tana matsayinta na biyu a Afirka kuma mataki na 21 a duniya.

A jerin sunayen da Fifa ta fitar ranar Alhamis, Argentina wacce ta kai wasan karshe a Copa America a bana tana matsayi na daya a duniya, sai Jamus a mataki na biyu Belgium ta uku a lissafin.

Brazil wacce ta karbi bakuncin kofin duniya a shekarar 2014 tana mataki na shida, yayin da Ingila ke matsayi na tara, sai Spaniya a mataki na 12 a iya murza leda a duniya.

Ga Jerin kasashe 10 da Fifa ta fitar na watan Yuli a nahiyar Afrika.

  1. Algeria
  2. Côte d'Ivoire
  3. Ghana
  4. Tunisia
  5. Senegal
  6. Cameroon
  7. Congo
  8. Cape Verde Islands
  9. Egypt
  10. Nigeria