Cabaye ya koma Crystal Palace daga PSG

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yohan Cabaye ya ci benci a PSG

Crystal Palace ta dauko Yohan Cabaye daga kungiyar Paris St-Germain ta Faransa a kan fan miliyan 10.

Dan kwallon Faransa mai shekaru 29, ya hade da kungiyar a yarjejeniyar shekaru uku.

Cabaye ya koma PSG ne daga Newcastle a kan fan miliyan 19 a watan Junairun 2014 amma wasanni 13 kacal aka soma da shi a kakar wasan da ta wuce.

A yanzu Cabaye ne dan kwallon da ya fi kowacce tsada a tarihin Crystal Palace.

Kocin Palace, Alan Pardew ne ya soma kawo Cabaye zuwa Ingila daga Lille a shekara ta 2011 a lokacin ya na kocin Newcastle.