Schweinsteiger da Schneiderlin sun hade da United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bastian Schweinsteiger da Morgan Schneiderlin

Manchester United ta kamalla dauko dan kwallon Jamus, Bastian Schweinsteiger da kuma dan Faransa Morgan Schneiderlin.

Schweinsteiger mai shekaru 30, ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru uku a kan fan miliyan 14.4 daga Bayern Munich.

Schneiderlin mai shekaru 25, shi ma ya koma United ne daga Southampton a kan fan miliyan 25.

Tuni United ta dauko Memphis Depay da kuma Matteo Darmian.

Schweinsteiger ya yi kwallo a karkashin kocin United Louis van Gaal a lokacin ya na jan ragamar Bayern daga 2009 zuwa 2011.