Capello ya raba gari da Rasha

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Capello ya sha suka a Rasha

Tsohon kocin Ingila, Fabio Capello ya raba gari da Rasha a matsayin kocin tawagar 'yan kwallonta bayan shafe shekaru uku a kan mukamin.

Dan shekaru 69, ya sabunta kwantaraginsa a shekara ta 2014 domin ya jagoranci Rasha zuwa gasar cin kofin duniya a 2018.

Amma an sallame shi saboda kasa samun sakamako mai kyau.

Rasha na da maki takwas daga wasanni shida a wasannin share fage na neman buga gasar cin kofin kwallon kasashen Turai.

An fitar da Rasha daga gasar cin kofin duniya a 2014 a Brazil ba tare da kasar ta samu nasara ko a wasa guda ba.

Rahotanni daga Rasha na cewar an ba shi euro miliyan 15 a matsayin diyya kafin a kore shi daga mukamin.